<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>27</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Yesu, na naɗa ka a cikin zuciyata.
 Ba wani iko ko'ina sai naka, Sarkina.
 Kai yaro ne a da tare da mu ka sha
 Jaraba, kai Mai Nasara, Yesu Mai Cetona.

[V2]
 2) Yesu, na naɗa ka a cikin zuciyata.
 Ba wani wanda na ke so shi amshi mulkinta
 Da zunubi kaɗai ya cika nawa rai,
 Amma yanzu na sani kai Ubangijina ne.

[V3]
 3) Yesu, na naɗa ka, ban rage kome ba,
 A bisa nawa duk da ni, sarauta za ka yi.
 Da goshinka ya sha azabar naɗin ƙaya,
 Yanzu ka ratsa mutuwa, ya kai Mai Nasara!

[V4]
 4) Yesu, an naɗa ka domin biyayyarka.
 Suna mafifici aka ba mai mulkin mutuwa.
 Yesu, ka cancanci ƙauna madauwamiya.
 An naɗa ka! An naɗa ka tun da har abada!

[V5]
 5) Allah ya naɗa ka Ɗansa Maɗaukaki.
 Baki ya kasa furtawa labarin girmanka.
 Gare ka ɗaukaka har abada,  Amin
 An naɗa ka! An naɗa ka! Immanuel Almasihu.</lyrics>
<title>Yesu, Na Naɗa Ka A Cikin Zuciyata LW27</title>
<author>Elvey, George Job (1816-1893), Bridges, Matthew (1800-1894), Thring, Godfrey (1823-1903)</author>
</song>